Qalibaf : lokacin nuna karfin iko da matsin lamba ya wuce

Kakakin majalisar dokokin Iran Mohamed Baqer Qalibaf ya kalubalanci Amurka akan keta yarjejeniyar fahimtar junar dake a tsakaninsu. Mista Ghalibaf ya yi Allah wadai da

Kakakin majalisar dokokin Iran Mohamed Baqer Qalibaf ya kalubalanci Amurka akan keta yarjejeniyar fahimtar junar dake a tsakaninsu.

Mista Ghalibaf ya yi Allah wadai da Amurka saboda keta yarjejeniyar yana mai jaddada cewa zamanin nuna karfin iko da matsin lamba ya wuce.

Da yake tsokaci kan keta yarjejeniyar da ta shafi mashigar Hormuz, ta hanyar sake sanya takunkumi kan fitar da man fetur na Iran, hare-haren da aka kai kan kudancin Iran, da kuma ci gaba da kai hare-haren sojojin Isra’ila a Lebanon, Ghalibaf ya tabbatar da cewa Washington ba za ta taba cika alkawuran ta ba in ji Kakakin Majalisar Dokokin Iran a shafinsa na Twitter.

“Lokacin lokacin nuna karfin iko da matsain lamba ya wuce in ji shi, sa’o’I bayan matakan Amurka na kai hare hare kan Iran.

Rundunar sojojin Amurka ta (CENTCOM) ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa sun “kai hari kan Iran a ranar 7 ga Yuli, inda suka kai hari kan wurare sama da 80 a Iran.”

A ranar 17 ga Yuni, Iran da Amurka ne suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna, wacce Pakistan ta shiga tsakani wadda ta tanadi dakatar da yaki gaba daya a dukkan fannoni, inda kuma bangarorin biyu sukayi alkawarin ci gaba da tattaunawa don cimma yarjejeniya ta karshe cikin kwanaki 60.

Dangane da tanade-tanaden wannan yarjejeniyar fahimta mai matakai 14, Iran na da alhakin tabbatar da cewa jiragen ruwa na kasuwanci za su iya wucewa kyauta na tsawon akalla kwanaki 60, yayin da za’a dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin teku cikin kwanaki 30.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted