Iran ta ce za ta dauki “matakai masu tsauri” don kare muradun kasarta duk da ci gaba da take yarjejeniyar fahimtar juna da Amurka ke yi.
Mataimakin Ministan Harkokin Waje kan harkokin Shari’a da Harkokin Ƙasashen Waje Kazem Gharibabadi ne bayyana hakan a cikin wani sako a shafin X, bayan da Amurka ta soke takunkumin da ya ba da damar sayar da man fetur na Iran, da kuma sabbin hare-haren da Amurka ke kai wa kan Iran.
Wannan shawarar ta zama “keta Mataki na 10 na takardar yarjejeniyar, yayin da ci gaba da kai hari ya zama keta Mataki na 1 da 2 na takardar yarjejeniyar fahimtar juna.
An sanya hannu kan takardar yarjejeniyar a watan da ya gabata da nufin kawo karshen yaki da Amurka da Isra’ila suka shelanta kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba tare da wani dalili ba.
Ta tanadi kuma dage takunkumin sayar da man fetur na Iran na tsawon kwanaki 60, yayin da sashe na farko ya buƙaci a dakatar da yaƙi a dukkan fannoni.