CNN: Cikin Sani Sojojin Amurka Su Ka Kai Wa Makarantar Minab Hari

Tashar talabijin din CNN ta nakalto wata majiya uku da take cewa, kwamandojin sojan Amurka sun yi watsi da gargadin da jami’an leken asiri su

Tashar talabijin din CNN ta nakalto wata majiya uku da take cewa, kwamandojin sojan Amurka sun yi watsi da gargadin da jami’an leken asiri su ka yi musu akan wuraren da za su kai wa hari a cikin Iran, su ka amince da kai wa makarantar “Minab” hari.

Harin na Amurka wanda bincike ya tabbatar da cewa ta kai shi ne da gangan, ya yi sanadiyyar shahadar  mutane 180 mafi yawancinsu kananan yara.

Rahoton ya kunshi cewa an gabatarwa da sojojin bayanai akan cewa da akwai bukatar sake bitar bagiren cibiyoyi da sansanin sojan da aka sani a baya gabanin a shigar da su a karkashin wuraren da za a kaiwa hari, kuma sai idan wani babban jami’in soja ya amince da hakan.

Sai dai kuma an yi watsi da wannan rahoton, da hakan ya haddasa kai hari mai hatsari akan makarantar kananan yara.

Bayan kai harin ne, manyan jami’an sojan na Amurka su ka fahimci ce, an kai shi ne akan wurin da ba tantance shi ba, wanda su ka yi watsi da rahotannin jami’an leken asiri.

A ranar 28 ga watan Febrairu ne Amurka ta kai wancan harin wanda ya ci rayukan dalibai ‘yan mata kanana su 168 sai 14 malaman makarantar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted