Tehran Tana Daukar Bakwancin Taron Bankwana Da Jagora Shahidi

Miliyoyin mutane daga ciki da wajen kasar Iran sun fara ciki birnin Tehran don halattar jana’iza da kuma bankwana da Imam Sayyid Aliyul Khaminaei Shahid

Miliyoyin mutane daga ciki da wajen kasar Iran sun fara ciki birnin Tehran don halattar jana’iza da kuma bankwana da Imam Sayyid Aliyul Khaminaei Shahid kuma jagoran juyin juya halin musulunci wanda aka fara gudanarwa a musallah Imam Khomainie (q) dake tsakiyar birnin.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya bayyana cewa a cikin kasashen dukkan bangarorin mutanen kasar kama daga yan kasuwa, malaman makarantu da Jami’o’iim malaman addini da da sauransu duk sun fara isowa birnin Tehran don halattan wannan jana’izar da kuma bankwana da Imam Asshahid.

Daga kasashen waje kuma tawagogi na masu makoki sun fara isa birnin tun jiya da kuma safiyar yau. Ana saran shuwagabannin kasashe da shugaban gwamnatoci daga kasashe kimani 30 da tawagar gwamnatoci fiye da 100 zasu halarci taron bankwanan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted