Qalibaf: Imam Khaminai(q) Yana Da Hakki A Kammu Gaba Daya

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya fadawa dawagar kasar Iraki da ta zo taron jana’iza da kuma bankwana na Shahid Ayatullahi Sayyid

Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibaf ya fadawa dawagar kasar Iraki da ta zo taron jana’iza da kuma bankwana na Shahid Ayatullahi Sayyid Aliyul Khamiei a nan Tehran kan cewa mutanen kasar Iran da Iraki da kuma sauran musulmi ya zama wajibi a garesu su kayaye wannan tafarkin da Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran.

Kamfani dillancin labaran ISNA na kasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a lokacinda yake tarban shugaban kasar Iraki Nechirvan Barzani shugaban kasar Iraki kuma wanda ya jagoranci tawagar kasar zuwa taron bankwana da kuma jana’izar na Imam Khaminaei a yau a nan Tehran.

Ya ce a cikin shekaru kimani 50 da suka gabata, Jagoran juyin juya halin musulunci, Imam sayyid Aliyul Khaminaei ya yi aiki wa addinin musulunci da musulmi, yayi wa mutanen duniya musamman marasa karfi aikin da ba zasu taba biyansa ba. Ladarsa sai Ubangijinsa, amma duk da haka mu kuma muyi kokarin bin tafarkinsa.

Dangane da yankin Qurdistan na kasar Iraki kuma, Qalibof yace Amurka da HKI sun so su yi amfani da lardin Kurdistan na kasar Iraki don cutar da Iran amma tare da hadin kai tsakanin hukumomin biyu ta kasa tabuka kome. Yace: Yana fatan wannan hadin kai zai ci gaba.

Daga karshe ya bayyana cewa, ci gaba da aiki tsakanin yankin da kuma kasar Iran zai hana wadan nan kasashe masharranta kara cutar da yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted