Mataimakin Shugaban Amurka Ya Ce A Shirye Suke Domin Tattaunawa Da Iran

Mataimakin shugaban kasar Amurka JD Vance ya bayyana cewa a shirye suke domin yin tattaunawa tare da Iran.
Mataimakin Shugaban Amurka Ya Ce A Shirye Suke Domin Tattaunawa Da Iran

Mataimakin shugaban kasar Amurka JD Vance ya bayyana cewa a shirye suke domin yin tattaunawa tare da Iran.

Vance ya bayyana hakan ne a lokacin da yake shirin birnin Washington domin kama hanyar zuwa birnin Islam-abad na Pakistan domin gudanar da tattaunawa tare da Iran.

Vance ya ce akwai wasu daga cikin sharuddan da Iran ta gindaya wanda da wuya Amurka ta amince da su, amma a cewarsa yana sa ran tattaunawar za ta yi armashi.

Tun kafin wanann lokacin dai Iran ta gindaya sharudda 10 wadanda tace dole ne Amurka ta amince da su kafin dakatar da yaki na makonni biyu, a kan amincewar Amurka da hakan ne a aka dakatar da yakin na tsawon makonni biyu.

Sai dai a nata bangaren Iran ta ce akwai batutuwa biyu wadanda ta bukata wadanda har yanzu ba a iawatar da su, wanda kuma rashin yin hakan zai iya sat a kauracewa tattaunawar, wadda ake sa ran gudanarwa a gobe Asabar a Islam-abad.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted