Iran na juyayin kwanaki 40 na shahadar Ayatollah Seyyed Ali Khamenei

Iran na juyayin kwanaki arba’in na shahadar jagoran juyin juya halin musulinci na kasar Ayatollah Sayyid Ali Khamenei. Tarukan juyayin sun hada da karatun al’kur’ani

Iran na juyayin kwanaki 40 na shahadar Ayatollah Seyyed Ali Khamenei

Iran na juyayin kwanaki arba’in na shahadar jagoran juyin juya halin musulinci na kasar Ayatollah Sayyid Ali Khamenei.

Tarukan juyayin sun hada da karatun al’kur’ani a cikin masalatai da kuma jerin gwano a manyan huraren haduwa a fadin kasar.

Haka zalika za’a ci gaba da tarukan a fadin kasar har zuwa ranar Juma’a a matakai daban daban.

A ranar 28 ga watan Fabarairu ne kawancen Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare haren ba gaire ba dalili kan Iran, wanda a yayinsa jagoran juyin juya halin Musulinci na kasar Ayatollah Sayyid Ali Khamenei tare da wasu makusantansa dama wasu manyan kwamandojin sojoji na kasar sukayi shahada bayan hari kan gidan jagoran da ofishinsa a Teheran.

Hare haren sun zo ne a daidai lokacin da Iran da Amurka ke tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted