Araghchi : ‘’ idan hare-hare sun tsaya, sojojinmu su ma zasu dakatar da hakan

Ya kuma bayyana cewa zurga zurga ta jiragen ruwa cikin aminci a mashigar ruwa ta Hormuz zata gudana cikin makonni biyu tare da hadin guiwa
Araghchi : ‘’ idan hare-hare sun tsaya, sojojinmu su ma zasu dakatar da hakan

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulinci ta Iran, Abbas Araghchi ya bayyana cewa idan hare haren kan kasarsa sun tsaya to jajirtatun sojojin kasar su ma zasu dakatar da kai hare hare.

Ya kuma bayyana cewa zurga zurga ta jiragen ruwa cikin aminci a mashigar ruwa ta Hormuz zata gudana cikin makonni biyu tare da hadin guiwa da sojojin Iran bisa tsari saboda halin da ake ciki.

Bayannin na ministan harkokin wajen Iran na zuwa ne a daidai sa’o’i kadan bayan sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon makonni biyu tsakanin Iran da Amurka.

Mista Araghchi, ya gode wa takwaransa na Pakistan Shehbaz Sharif, da kuma babban kwamandan sojojin Pakistan Marshal Asim Munir akan jan kokarin da sukayi wajen ganin an kawo karshen yaki a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted