Pakistan zata karbi bakuncin tattaunawa tsakanin Iran da Amurka

Shehbaz Sharif, ya wallafa hakan a shafinsa na ‘’X’’ cewa : cikin babban farin ciki ina sanar da cewa Jamhuriyar Musulinci ta Iran da kuma
Pakistan zata karbi bakuncin tattaunawa tsakanin Iran da Amurka

Fira ministan Pakistan ya sanar da mika gayyata ga kasashen Iran da kuma Amurka zuwa ga tattaunawa a ranar Juma’a bayan amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta.

Shehbaz Sharif, ya wallafa hakan a shafinsa na ‘’X’’ cewa : cikin babban farin ciki ina sanar da cewa Jamhuriyar Musulinci ta Iran da kuma Amurka, da kuma kawayensu sun amince da tsagaita wuta nan take a dukkan fagegen yaki ciki har da Liban da kuma sauren yankuna.

Tsagaita wutar ta fara aiki daga misalin karfe 3 :30 na safiyar Laraba 8 ga watan Afrilu 2026 agogon Iran, karfe 20h00 na ranar Talata agogon tsibirin gabashin Amurka.

Ya kara da cewa ina jinjinawa matsayar da jagororin wadanan kasashen suka cimma kuma ina gayyatar tawagogin kasashen biyu dasu zuwa Islamabad a ranar Juma’a 10 ga watan Afrilu domin cimma yarjejeniya ta karshe da zummar warware dukkan sabanin dake akwai.

Kuma dukkan kasashen biyu sun nuna da gaske su ke wajen cimma yarjejeniyar fahimtar juna da zata kai ga samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted