London: Zanga-Zangar Neman Kawo Karshen Yaki A Kan
An gudanar da gagarumar zanga-zangar neman kawo karshen yakin Amurka da Isra’ila a kan kasar Iran a birnin Landan na kasar Burtaniya.
Rahotanni sun ce an gudanar da jerin gwanon ne a birnin Landana daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da ire-irensa a kasashe daban-daban na nahiyar turai da ma wasu kasashen duniya, domin yin Allah wadai da hare-haren Amurka da Isra’ila a kan Iran.
Wannan jerin gwanon dai ya kunshi kungiyoyin kare hakkin bil adama da kuma kungiyoyin masu adawa da yaki, wadanda suke fafutuka domin samun zaman lafiya a duniya.
Haka nan kuma sun yi kira da a dakatar da yakin nan take, tare da daukar matakan da suka dace a kan wadanda suka tayar da wannan tarzoma.