Aref: Goyon Bayan Al’umma Ne Ya Wanzar Da Juyin Juya Hali A Iran

Mataimakin shugaban kasar Iran Reza Aref ya bayyana cewa, juyin juya halin muslunci a kasar yana ci gaba da kasacewa ne bisa goyon bayan al’ummar
Aref: Goyon Bayan Al’umma Ne Ya Wanzar Da Juyin Juya Hali A Iran

Mataimakin shugaban kasar Iran Reza Aref ya bayyana cewa, juyin juya halin muslunci a kasar yana ci gaba da kasacewa ne bisa goyon bayan al’ummar kasar.

Aref ya jinjina wa al’ummar Iran kan yadda suke fitowa kullum rana kwansu da kwarkwatarsu suna yin Allawadai da harin da aka kaddamar a kan kasarsu.

Ya ce wannan goyon bayan tare da tsayin dakan al’umma da kuma turjiya ta dakaru da ke fagen daga su ne babban sirrin wanzuwar juyin.

Ya ci gaba da cewa, makiyan kasar Iran sun jahilci al’ummar wannan kasa, domin kuwa suna tunanin cewa ta hanyar kasha jagorori kasar za ta rushe, amma abin da ya faru akasin haka ne.

Sannan kuma yadda wajabcin ajiye sabani na siyasa ko fahimta a gefe guda, tare da fifita maslahar kasa a kowane lokaci, wanda kuma shi ne zai kara tabbatar da hadin kan al’ummar kasar domin tunkarar kalubale.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted