Daruruwan mutane sun gudanar da jerin gwanon nuna goyon baya ga Iran a birnin Vienn na kasar Austria.
A ci gaba da gudanar da jerinm gwano a kasashen duniya domin yin Allah wadai da hare-haren Amurka da Isra’ila a kan Iran, an gudanar da jerin gwano a birnin Veinna na kasar Austria.
Wannan jerin gwanon dai ya kunshi kungiyoyin kare hakkin bil adama da kuma kungiyoyin masu adawa da yaki, wadanda suke fafutuka domin samun zaman lafiya a duniya.
Haka nan kuma sun yi kira da a dakatar da y kin nan take, tare da daukar matakan da suka dace a kan wadanda suka tayar da wannan tarzoma ta hanyar kaddamar da hari kan kasar Iran