Babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon Sheikh Naeen Qasem ya bayyana cewa, Iran tana yakin girman duniya nev baki daya a madadin dukkanin kasashen musulmi da sauran kasashe masu ‘yanci da sauran raunana na duniya.
Sheikh Naeem Qasem ya bayyana hakan ne a yau a cikin wani jawabinsa dangane da halin da ake ciki nay akin da Amurka da Isra’ila suka kaddamar a kan kasar Iran da nufin rusa tsarin gwamnatin musulunci a kasar.
Ya ce tabbas abin da yake faruwa yaki ne tsakanin karya da gaskiya babu wani abu bayan haka, kuma kungiyar Hizbullah a nata bangaren tana kan bakanta na kare kasar Lebanon daga yunkurin mamaye kasar da shinfida ikon Isra’ila a kanta, kuma a shirye take ta yi sadaukarwa mafi girma domin ci gaba da tunkarar wannan mummunar manufa ta yahudawa a kan Lebanon da al’ummarta.