Iran: An Rataye Wani Mutum A Yau Bisa Laifin Yi Wa Isra’ila Leken Asiri

A yau 18 ga watan Maris 2026, hukumomin tsaro a Iran sun rataye wani mutum bayan da kotu ta same shi da laifin yi wa
A yau 18 ga watan Maris 2026, hukumomin tsaro a Iran sun rataye wani mutum bayan da kotu ta same shi da laifin yi wa Isra’ila ayyukan liken asiri a cikin kasar.

A yau 18 ga watan Maris 2026, hukumomin tsaro a Iran sun rataye wani mutum bayan da kotu ta same shi da laifin yi wa Isra’ila ayyukan liken asiri a cikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim ya bayar da rahoton cewa, mutumin mai suna Koroush Kivani, an kama shi ne dauke da wasu na’urori na musamman na aikewa da bayanan sirri, wadanda yake amfani da su domin aikeawa da bayanai ga jami’an hukumar liken asiri ta Isra’ila Mossad,

kamar yadda kuma aka samu kudi kimanin euro 30,000 tare da shi.Ya amsa cewa yana aiki tare da wasu jami’an Mossad wadanda ya hadu da su ta hanyar shafukan zumunta,

kuma a hankali a hankali suka janwo a jikinsu , har ma suna haduwa a wajen kasar Iran, haduwa ta karshe da suka yi ita ce a birnin Berlin na kasar Jamus.

Ya amsa cewa ya aike musu da bayanai da kuma hotuna na wurare masu muhimmanci ta fuskar tsaron kasa a Iran.An rataye shi a da safiyar yau bayan kotu ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted