Sakataren Majalisar Koli Ta Tsaron Kasa A Iran Dr. Ali Larijani Ya Yi Shahada

Babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasa a Iran Dr. Ali Larijani ya yi shahada, a wani da jiragen yakin Amurka da Isra’ila kai masa a Tehran.

Larijani ya taka muhimmiyar rawa a tsawon shekaru a kasar Iran tun bayan samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar.
Daga cikin mukaman da ya rike hard a shugaban hukumar rediyo da talabijin na kasar Iran na tsawon shekaru masu yawa, haka nan kuma ya taba rike mukamin shugaban majalisar tsaron kasar a lokacin mulkin Ahmadinejad.