Yawan karfen da kasar Iran take samarwa ya karu da kashi 15% a wannan shekara ta 2026 zuwa ton miliyon 2.6 kamar yadda kungiyar masu samar da karafa a duniya ta bayyana.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hakan na faruwa ne a tsakiyar takunkuman tattalin arziki mafi muni wadanda kasashen yamma suka dorawa JMI.
Samar da karafa dai yana daga cikin manya-manyan hanyoyin da kasar Iran take tallafawa ayyukan ci gaban kasa, a cikin kasa da tallafawa manya-manyan kamfanoni da kuma samun kudade shiga daga kasashen waje.
Labarin ya kara da cewa, samar da karfe a cikin gida yana daga cikin al-amura da suka taimakawa kasar Jurewa takunkuman tattalin arziki mafi muni wadanda kasashen yamma suka dorawa kasar.