Sojojin Ruwan Iran Sun Dawo Daga Atisaye Tare Da Alwashin Kare Kasar Da Rayukansu

Sojojin ruwa na kasar Iran runduna ta 103 ta dawo daga rangadin ruwayen kasa da kasa bayan dadewa na tsawon kwanaki 100 a cikinsu. Tashar

Sojojin ruwa na kasar Iran runduna ta 103 ta dawo daga rangadin ruwayen kasa da kasa bayan dadewa na tsawon kwanaki 100 a cikinsu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kwamandan rundunar Admiral Emad Nejad Moridi ya bayyana cewa wannan aikin ya kaisu wurare da dama wadanda suka hada da kasar Afirka ta kudu inda suka shiga atisayen sojojin ruwa tare da kasashe har guda 9.

Labarin ya kara da cewa, jiragen ruwan yaki mai suna Makran da Shahid Naqdi da kuma Shahid Mahdavi na rundunar IRGC mai daukar jirgin sama mai saukar ungulu.

Tun cikin watan Decemba ne rundunar ta kama hanya ta shiga ruwayen kasashen duniya inda ta isa har kasar Afirka ta kudu don daga tutar Iran a kasashen duniya da kuma tabbar masu sakon zaman lafiya daga kasar Iran. Tafiyar dai, zuwa da dawowa duk sun kai kilomita 13,000 na ruwa.

Daga karshe babban kwamandan sojojin ruwa na kasar Iran Admiral Irani wanda ya yi jawabi a bikin tarban rundunar a tashar jiragen ruwa na birnin Konarak a yau.yace shiga cikin atisayen Afrika ta kudu da rundunar tayi ya aika da sako mai kyau na jmi ga kasashen duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted