A kalla ‘yan hijira 8,000 ne su ka mutu da kuma bacewa a duniya a cikin shekarar 2025 da ta wuce, bisa rahoton hukumar MDD dake kuma da ‘yan hijira.
Rahoton ya bayyana ibtila’in da ya fada wa ‘yan hijrar a shekarar ta 2025 da cewa, wata babbar gajiyawa ce da duniya ta nuna.
Kididdigar ta MDD ta ce, adadin mutanen da aka tabbatar da mutuwarsu da kuma bacewarsu shi ne 7,667. Mutanen da suke fitowa daga nahiyar Afirka suna ratsawa ta tekun Mediterranea da ruwan ya cinye su, sun kai 2,108, a 2025, sai kuma wasu 1,047 da su ka yi kokarin isa kasar Spain a tsibirin “Canary” kamar yadda bayanan su ka nuna.
A farkon watanni biyun nan na 2026 ma an sami mutuwar mutane da dama da suke kokarin yin hijira, daga cikinsu da akwai wasu 600 a tekun Meditrenia a ranar Talatar da ta gabata.
Babbar Darakta ta kungiyar ‘Hijira ta kasa da kasa, Amy Pope ta bayyana cewa; wadannan mace-macen za a iya hana faruwarsu, tana mai yin kira da a rika bin hanyoyin da suke halartattu.
Haka nan kuma ta ce, dakatar da bayar da kudade da takuranawa kungiyoyin aikin ceto da agaji da ake yi, da kayyade hanyoyin tattara bayanai su ne muhimman matsalolin da ake fuskanta.
A cikin makwanni biyu da su ka gabata kuwa, ruwa ya ci wasu mutane 23 a tsakanin ruwan kasashen Italiya da Libya, yayin da wasu daruruwa su ka bace a wannan yankin.