Shugaba Masoud Pezeshkian ya yi watsi da ikirarin da shugaban Amurka Donald Trump ya yi game da adadin wadanda suka rasa rayukansu a tarzomar da aka yi a Iran kwanan nan, yana mai cewa duk wani shakku game da bayanan hukuma a Tehran to dole ne ya kasance a kan hujjoji ba shaci-fadi ba.
Da yake magana da jami’an lardin Mazandaran a ranar Alhamis, Pezeshkian ya mayar da martani kan ikirarin shugaban na Amurka cewa an kashe mutane 32,000 a zanga-zangar watan Janairu, inda ya kara da cewa an fitar da kididdigar hukuma game da wadanda abin ya shafa, gami da lambobin shaidarsu na kasa. Ya kuma jaddada cewa duk wanda ke zargin cewa adadin wadanda suka mutu ya fi haka, dole ne ya kawo hujjoji a rubuce, su wane sunayensu da kuma lambobinsu na ‘yan kasa.
Shugaban ya kuma lura cewa sama da 2,000 daga cikin wadanda abin ya shafa jami’an tsaro ne da kuma mutanen gari wadanda basu daga cikin masu tayar da tarzoma.
Ofishin shugaban kasar ya fitar da sunayen mutane 2,986, wadanda suka rasa rayukansu wadanda hukumar lafiya ta Iran ta tattara tare da sake duba su tare da hadin gwiwa da hukumar rajistar jama’a ta kasa a Iran, a wani bangare na tantance kididdiga ta gaskiya kan hakikanin wadanda suka rasa rayukansu.
Pezeshkian ya bayyana cewa, a cikin tarzomar da ‘yan ta’adda da ke samun goyon bayan kasashen waje suka tayar a baya-bayan nan, sun kona masallatai sama da 350 da makarantu 300, inda ya siffanta irin wadannan ayyuka a matsayin yunkurin kifar da gwamnati, ba zanga-zangar lumana ba ba.