A makon da ya gabata ne ministan man fetur da gas na kasar Iran Muhsen Paknejad ya bada sanarwan cewa, kasarsa ta wuce sauran kasashen yankin hakar iskar gas a filin hakarsa da ke yankin Pars ta kudu wanda shi ne filin hakar gas na tarayya mafi girma a duniya.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan na faruwa ne a dai dai lokacinda kasar take fuskantar takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kasar daga Amurka da wasu kasashen yamma.
Wannan filin hakar iskar gas yana kan iyakar kasar Iran da Qatar kuma kasashen yankin sun dade suna gasa a tsakaninsu kan hakar iskar gas mafi yawa. Kafin haka dai kasar Qatar wace take samun goyon bayan kamfanonin hakar gas na manya-manyan kasashen duniya, tana gaban kowa yawan iskar gas da take haka a yankin, amma a cikin yan shekarun da suka gabata Iran ta zo ta wuce dukkan makobtanta a hakar iskar.
Kwarewar masana na kasar Iran a aikin hakar ya yi tasiri wajen kaita wannan matsayin inji rahoton.
Iran tana samarda kasha 70% na yawan iskar gas wanda kasar take samarwa, sannan daga nan ne ake samarda kashi 40% na gasoline. Fadada wannan filin hakar gas ya taimakawa kasar wajen samun wadata da kuma yenci daga dogaro da wani don samun irin wannan makamashi.
Iran dai tana da kamfanonin sarrafa iskar gas har 13 tare da shimfida bututu mai fadin inci 32 na tsawo kilimita 3,200. Sannan tana da wuraren ajiyar gas har 39 a kasar. Wadan nan gaba daya suna samar da cubic mita miliyon 730 na iskar gas a ko wace rana. Iran tana samun kudaden shiga har na dalar Amurka biliyon $3.5 a ko wace shekara a wannan filin kadai.