Kakakin Gwamnatin Iran Tace: Iran Ta Fi Son Diblomasia Kan Yaki

Iran ta fi son diblomasia kan yaki, amma kuma tana daukar biyun a matsayin zabi don kare muradon kasar. Kamfanin dillancin labaran Iranpress ko IP

Iran ta fi son diblomasia kan yaki, amma kuma tana daukar biyun a matsayin zabi don kare muradon kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iranpress ko IP ya nakalto Fatemeh Mohajirani kakakin gwamnatin JMI tana fadar haka a yau Talata ta kuma kara da cewa, kamar yadda sojojin kasar suke cikin shiri, kamar yadda kowa ya gani a rawanda dajin da suka gudanar, suke kuma ci gaba da gudanarwa, hakama hanyar diblomasiyya ma tana tafiya da karfinta, muna kuma sanya ida kan abubuwan da suke kaiwa su komo a bangarorin biyu.

Kafin tada hankali na baya bayan nan dai Amurka da HKI sun farwa kasar Iran da yaki na tsawon kwanaki 12 daga ranar 13 ga watan Yunin shekara ta 2025. Inda suka kashe manya-manyan jami’an sojojin kasar, da masana fasahar Nukliya da kuma sauran mutanen gari, wanda adadindu ya kai fiye da mutum dubu guda.

Sannan bayan juyin mulkin da suka shirya a ranar 8 ga watan Jenerun da ya gabata a kasa maiwa ga manufa, gwamnatin kasar Amurka a halin yanzu ta jibge sojojinta kusa da tekun farisa da nufin farwa kasar Iran da yaki, da kuma sauya shugabancin kasar.

A halin yanzu dai akwai yiyuwar amurka ta farwa kasar Iran da yaki a ko wani lokaci, duk da cewa ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana shirin halattar zagaye na uku na tattaunawa kan shirin nukliyar kasar ta Iran a birnin Geneva a ranar Alhamis mai zuwa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted