Iran ta bukaci Amurka ta girmama diflomasiyya maimakon amfani da yaki da takunkumi

Iran ta bukaci Amurka ta girmama hanyar diflomasiyya maimakon amfani da barazanar yaki, da takunkumi. Mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar kan Shari’a da Harkokin Kasashen

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen Iran Kan sha'anin Shari'a da Harkokin ketare,

Iran ta bukaci Amurka ta girmama hanyar diflomasiyya maimakon amfani da barazanar yaki, da takunkumi.

Mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar kan Shari’a da Harkokin Kasashen Waje Kazem Gharibabadi ya ce lokaci ya yi da Amurka za ta yi watsi da takunkumin da ba shi da amfani da kuma manufofin yaki da Iran da suka gaza cimma komai, yana mai kira da a girmama diflomasiyya a matsayin hanya daya tilo da za a bi.

“Makiyan Iran na iya fara yaki, amma ba za su iya tantance karshensa ba,” Kazem Gharibabadi a jawabinsa a Majalisar Kare Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya a Geneva.

Ya ce ‘yan Iran ba sa neman kai hari kan wasu kasashe amma za su tsaya tsayin daka kan duk wani matakin soja ko siyasa kan Jamhuriyar Musulunci kuma za su kare kasarsu.

Tun a farkon watan Janairu ne Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar daukar matakin soja kan Iran, bayan goyon bayan da ya bai wa zanga zangar da ta rikide zuwa tarzoma a Iran sakamakon ingizo na kasashen waje.

Tun daga lokacin ne Trump ya ba da umarnin girge manyan jiragen ruwan soji  da na sama a kusa da Iran, kuma ya yi gargadin kai hare-hare idan Tehran ba ta amince da sharuddan dake kunshe a yarjejeniyar da Amurka ta gabatar ba.

Iran dai na mai nanata cewa a shirye take ta cimma yarjejeniyar da zata amfani kowa da kowa, amma kuma a shirye take ta maida kakkausan martini idan an abka mata da yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted