Jakadan Amurka a Faransa ya ki amsa kiran da minisan harkokin wajken Faransa ya yi masa a birnin Paris kan wasu kalammai da shugaban Amurka Donald Trump ya furta game da mutuwar wani matashi a faransa.
Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Noël Barrot ya nemi a dakatar da damar da jakadan Amurka Charles Kushner ke da ita na ganawa da ministocin gwamnati faransa kai tsaye bayan ya ki amsa kiran da aka masa game da mutuwar Quentin Deranque.
Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta kira jakadan Amurka Charles Kushner amma ya ki zuwa zaman da aka tsara da karfe 7 na yamma a ranar Litini in ji ma’aikatar.
Wannan rashin halartar ya biyo bayan cece-kucen da suka faru sakamakon kalaman gwamnatin Trump kan mutuwar matashi Quentin Deranque a gefen zanga-zangar da aka gudanar a ranar 12 ga Fabrairu a birnin Lyon.
A cikin wata sanarwa, Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta yi Allah wadai da “rashin fahimtar ainihin aikin jakada, wanda ya kunshi wakiltar kasarsa.
” Saboda haka, Jean-Noël Barrot ya yanke shawarar cewa Charles Kushner “ba zai sake samun damar shiga kai tsaye ga membobin gwamnatin Faransa ba.
Washington ta yi Allah wadai da tashin hankalin siyasar a faransa kuma ta yi kira da a gurfanar da wadanda ke da alhakin a gaban kuliya, Matakin da Paris ta yi kakkausar suka a kai tana mai cewa “Ba ta yarda da duk wani amfani da lamarin ba don cimma burin siyasa,” in ji Jean-Noël Barrot.