A yau Litinin an sake bude iyakar kasashen DRC da Brundi bayan da ta dauki watanni a rufe, sanadiyyar hare-haren kungiyar M23 dake samun goyon bayan Burundi.
Iyakar ta Kavimvira dake a kusa da tafkin Tanganyika tana da matukar muhimmanci ta fuskar kasuwanci wacce kuma take hada birnin Bujumbura da kuma yankin Uvira.
An rufe wannan mahsigar ne dai a watan Disamba da kungiyar M23 ta fara kai wa garin Uvira hari.
Dubban mutane ne dai su ka gudu daga wannan yankin zuwa kasar Burundi a lokacin da kae fada.
Sai dai bayan da kungiyar ta M 23 ta janye daga garin na Uvira a watan Janairu, an sake bude tattaunawa a tsakanin kasashen biyu domin a bude wannan iyaka.
A halin yanzu dai sojojin DRC sun sake shimfida ikonsu a cikin garin, kamar yadda gwamnan Kivu ta Kudu Jean Jacques Purusi ya ambata.
A Yau Litinin na misalin 8:00 ne aka sanar da bude wannan iyakar ta kasashen biyu.
Yankin gabashin kasar DRC dai yana cike da albarkatun karkashin kasa da ma’adanai da manyan kamfanonin duniya suke nema. Tsawon shekaru 30 kenan da yankin na gabashin DRC yake fama da fadace-fadace a tsakanin kungiyoyin da suke samun taimako daga kasashen waje masu son wawason albarkatun wannan kasar.