Gwamnatin Sudan ta yi kakkausar suka ga shugaba Yoweri Museveni na Uganda bayan da ya karbi bakoncin jagoran mayaƙan RSF Mohamed Hamdan Dagalo a Kampala a kokarin lalubo hanyoyin magance rikicin Khartoum na kusan shekaru 3, wanda ya tagayyara iyalai fiye da miliyan 11 tare da kisan dubban daruruwan fararen hula.
Cikin sanarwar da gwamnatin Sojin ta Sudan ta fitar karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan ta bayyana cewa Uganda bata da hurumin katsalandan a rikicinta.
Gwamnatin ta nuna bacin rai matuka kan yadda shugaba Museveni ya karbi bakon Dagalo wanda ta ce ya sabawa dokokin kasa da kasa kasancewar jagoran na RSF mai laifi da ke dakon hukunci.
Kafin yanzu kasashe da dama sun nemi shiga tsakani don warware wannan yaki na kusan shekaru 3 amma suna haduwa da kakkausar suka daga Sudan, ciki kasashen kuwa har da Habasha wadda gwamnatin Sojin ta Sudan ta bayyana da me goyon bayan mayakan RSF. A baya-bayan nan Saudiya da kanta ta bukaci Amurka ta shiga tsakani don warware wannan yaƙi da ke matsayin mafi muni da Sudan ta gani a tarihi.