Hezbollah ta ce ba ta da wani zabi illa ta kare kanta bayan hare-haren Isra’ila

Kungiyar Hezbollah ta Lebanon, tace ba ta da wani zabi illa ta kare janta bayan munanen hare haren da Isra’ila ta kai wanda ya yi

Kungiyar Hezbollah ta Lebanon, tace ba ta da wani zabi illa ta kare janta bayan munanen hare haren da Isra’ila ta kai wanda ya yi sanadin shahadar wasu daga cikin mambobinta.

Mahmoud Qamati, mataimakin shugaban majalisar siyasa ta Hezbollah, a cikin wani jawabi da gidan talabijin na al-Manar na Hezbollah ya watsa ya ce kungiyar “ba ta da wani zabi” illa ta kare kanta bayan hare-haren Isra’ila mafi muni a gabashin Lebanon inda ta kashe membobin kungiyar takwas, ciki har da babban kwamandan Æ™ungiyar Hussein Mohammed Yaghi.

Daya daga cikin jami’an Hezbollah ya ce uku daga cikin wadanda suka mutu kwamandojin yankin ne kuma ya bayyana su a matsayin Ali al-Moussawi, Mohammed al-Moussawi, da Hussein Yaghi.

Yaghi dan Mohammed Yaghi ne, wani fitaccen jami’in Hezbollah kuma daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar, wanda ya mutu a shekarar 2023.

Mohammed Yaghi shi ma wani mataimaki ne na kusa da marigayi shugaban kungiyar Hizbollah Sayyed Hassan Nasrallah, wanda aka kashe a wani harin sama da Isra’ila ta kai a kudancin Beirut a watan Satumbar 2024.

Ma’aikatar Lafiya ta Lebanon ta ce hare-haren Isra’ila a gabashin Lebanon sun kashe mutane 10 tare da raunata 24, ciki har da yara uku, wanda ya nuna yadda Isra’ila ke ci gaba da keta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a watan Nuwamban 2024 da Isra’ila

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted