Araqchi Ya Mayar Da Martani Kan Maganganun Donald Trump Shugaban Amurka

Ministan harkokin wajen Iran ya mayar da martani ga ikirarin shugaban Amurka yana cewa: Ya yi magana da hujja Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi,

Ministan harkokin wajen Iran ya mayar da martani ga ikirarin shugaban Amurka yana cewa: Ya yi magana da hujja

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi, wanda ke mayar da martani kai tsaye ga kalaman Shugaban Amurka Donald Trump, ya jaddada cewa duk wanda ke kokwanton sahihancin bayanan Iran dole ne ya bayar da shaida.

Araqchi ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa: “Domin cika alkawari ga al’ummar na tabbatar da gaskiya, gwamnatin Iran a baya ta buga cikakken jerin dukkan wadanda harin ta’addanci ya shafa 3,117, ciki har da kimanin jami’an tsaro 200.”

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: “Idan wani yana shakkar ingancin maganganun gwamnatin Iran, to a yi magana da shaidu.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted