Kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kimanin Falasdinawa 5,000 ne suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren tsagerun yahudawa ‘yan kaka gida a Yammacin Kogin Jordan
Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Stéphane Dujarric a ranar Juma’a cewa: “Hare-haren tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida a Yammacin Kogin Jordan sun raba kimanin iyalai 880 na Falasdinawa ko kuma sama da mutane 4,700 ” da matsugunansu.
Dujarric ya kara da cewa: “Abokan aikinsu na agaji sun yi gargadi game da ci gaba da tashin hankali da sauran ayyukan tilastawa da sojojin mamayar Isra’ila da tsagerun ‘yan sahayoniyya mazauna yankin suka yi, wanda ya haifar da hasarar rayuka, hasarar dukiyoyi, da kuma tilastawa mazauna yankin Yammacin Kogin Jordan barin muhallinsu.
Mai magana da yawun babban saataren ya ce “tsakanin 3 da 6 ga Fabrairu, sojojin mamayar Isra’ila sun kashe Falasdinawa uku, wanda ya kawo jimillar wadanda suka yi shahada a wannan shekarar zuwa tara, ciki har da yara biyu. An kuma samu akalla hare-hare 86 da tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida suka kai a wannan lokacin, wanda ya haifar da raunuka ga Falasdinawa sama da 60 da kuma korar wasu 146.”