Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce duk wani mataki da za’a dauka game da Gaza dole ya dakatar da hare-haren Isra’ila.
Hamas ta kuma yi Allah wadai da kiran “Majalisar Zaman Lafiya” kan Gaza na Amurka.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hamas ta tabbatar da cewa duk wata shawara ko yarjejeniya ta siyasa game da Gaza dole ne ta dogara ta dakatar hare-haren Isra’ila gaba daya.
Ta kuma sake nanata bukatar tabbatar wa Falasdinawa ‘yancinsu na cin gashin kai.
” Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta yi kira ga masu shiga tsakani da su tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta yadda ya kamata.
A ranar Alhamis ne, Shugaban Amurka Donald Trump ya jagoranci taron farko na “Majalisar Zaman Lafiya” a Washington, a Cibiyar Zaman Lafiya ta Amurka.
Taron ya mayar da hankali ne kan mataki na gaba na tsagaita wuta mai rauni a Gaza, da sake gina yankin bayan yakin, da sauran abubuwan da Trump ya gabatar na shirin zaman lafiya mai gabobi 20 ga yankin.
Kasashen mambobin sun yi alkawarin sama da dala biliyan 7 na agaji da sake gina Gaza, kuma Trump ya sanar da karin gudummawar dala biliyan 10 daga Amurka.
Wasu kasashe sun kuma yi alkawarin samar da sojoji ga rundunar tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa da aka tsara don Gaza.