Shugaba Masoud Pezeshkian na Iran ya ce kammala yarjejeniyar hadin gwiwa na tsakanin kasar da Rasha zai bude “sabon babi” da kuma babban ci gaba a cikin kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Mista Pazehskian ya bayyana hakan ne a yayin da karbi wata tawagar kasar Rasha da ministan makamashi na kasar, Sergei Tsivilev, ke jagoranta a Tehran.
Shugaban Iran, yana mai cewa aiwatar da yarjejeniyoyin a fannin sufuri, makamashi, mai da iskar gas, noma, kayayyakin abinci, da tsaro abu ne mai kyau.
“Mun kuduri aniyar aiwatar da wannan takardar [haɗin gwiwa ta dabarun] domin cin moriyar juna.
Shi kuwa a nasa bangare Ministan Rasha ya yi wa shugaban Iran bayani game da sakamakon Kwamitin Haɗin Gwiwa na 19 na Tattalin Arziki, na tsakanin kasashen.
M.Tsivillev ya jaddada zurfin haɗin gwiwar, yana mai cewa Rasha tana daukar dangantakarta da Iran a matsayin babban abun fifitawa.
Ya ce shekarar da ta gabata ta kasance mai amfani musamman ga dangantakar kasashen biyu.