Yan Sanda Isra’ila Sun Zafafa Kai Hare-hare A Masallacin Qudus

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an yan sanda HKI sun tsananta kai hare-hare a masallacin Qudus kuma zai ci gaba a tsawon wata guda na Azumin

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an yan sanda HKI sun tsananta kai hare-hare a masallacin Qudus kuma zai ci gaba a tsawon wata guda na Azumin watan Ramadan kamar yadda gwamnatin sahyuniya ta sanar da fara tsananta bincike a harabar masallacin.

Arad Braverman wani babban jami’in yan sandan isra’ila a birnin kudus yace zaa baza jami’an tsaro dare da rana a fadin yankunan dake kewaye da birnin Kudus, kuma dubban sojojin isra’ila za su kasance cikin shiri a lokacin sallar juma’a da musulmi masu ibada ke halartar

haka zalika hukumomin Isra’ila sun dauki matakin hana matasa faladinawa shiga masallacin Kudus a lokacin watan Ramadan ,kuma za ta tsananta wajen shigar masu ibada dake fitowa daga gabar yammacin kogin Jodan da sauran yankunan da aka mamaye.

majiyar labaran hukumomi a birnin Kudus sun ce an sanar da su cewa za’a bada izinin shiga ga wasu tsirarun mutane ne ga mazaje da suka haura shekaru 55 da kuma mata da suka haura shekaru 50, kamar yadda aka yi a shekarar da ta wuce.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted