Kasashen Nijar Da Aljeriya Sun Sanar Da Bude Sabon Shafi A Cikin Alakarsu

Shugaban mulkin soja na jamhuiryar Nijar, Janar Abdurrahman Tiani wanda ya kai ziyarar aiki kasar Aljeriya ya sanar da bude sabon shafi a alaka da

Shugaban mulkin soja na jamhuiryar Nijar, Janar Abdurrahman Tiani wanda ya kai ziyarar aiki kasar Aljeriya ya sanar da bude sabon shafi a alaka da kasar.

Janar Abdurrahman Tiani ya gana da takwaransa na kasar Aljeriya, Abdulmajid Tebbani a birnin Alges a jiya Litinin inda su ka tattaunawa batun shimfida bututun iskar Gas.

A nashi gefen Tabbubi ya ce, ziyarar ta shugaban kasar Nijar ta kawo karshen yanayin da ba a saba da shi ba a tsakanin kasashen biyu.

A cikin watan Aprilu na shekarar 2025 kasar Aljeriya ta harbo jirgi maras matuki na kasar Mali, da hakan ya jawo tabarbarewar alaka a tsakaninta da kasashen na Mali, Jamhuiryar Nijar, da Burkina Faso da suke da kawance.

Kasashen uku sun kirayi jakadunsu daga birnin Alges bayan wancan abinda ya faru.

Sabon bututun da za a shimfida zai ratsa kasahsen Aljeriya, Jamhuriyar Nijar da Nigeria. Bayan watan Ramadan ne ake sa ran dora harsashin fara wannan aikin.

Tsawon bututun da za a shimfida zai kai kilo mita 4,000 wanda zai rika dauko Gas, daga Nigeria, ya ratsa ta jamhuriyar Nijar, sannan ya dire a kasar Aljeriya.

Aikin ya yin isa a cikin 2025, kafin ya sami tsaiko saboda sabanin da ya kunno kai a tsakanin kasashen na Sahel da kasar Aljeriya.

Bayan ganawar ta Jiya Litinin, shugaban kasar ta Ajeriya ya yi alkawalin taimakawa jamhuriyar Nijar da sami sauki daga matsalolin tattalin arzikin da take fuskanta,musamman a cikin fagagen kiwon lafiya da ilimi.

 A makon da ya shude dai Aljeriya ta aike da tawaga zuwa cikin kasar Burkina Faso domin tattauna hanyoyin hakar ma’adanai. Sai dai kums har yanzu ba ta warware sabani da kasar Mali ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted