Iran Ta Soki Gwamnatin Kasar Amurka Kan Kara Takurawa Kasar Cuba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya tir da gwamnatin kasar Amurka kan kara takurawa gwamnatin kasar Cuba da take yi, bayan takunkuman tattalin arzikin

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya tir da gwamnatin kasar Amurka kan kara takurawa gwamnatin kasar Cuba da take yi, bayan takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar shekaru fiye da 60 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Esmail Baghaei kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran yana fadar haka a jiya Litinin, ya kuma kara da cewa, takunkuman Amurka a kan kasar ta Cuba basa kan doka, kuma sabawa dokokin kasa da kasa na kare hakkin bil’adama ne.

Ya kuma bayyana goyon bayan gwamnati da mutanen kasar Iran ga mutanen kasar Cuba wadanda aka zalunta.

Kasashen duniya da dama da kuma kungiyoyin kasa da kasa sun nuna damuwarsu da yadda gwamnatin shugaba Trump ta kara takurawa kasar ta Cuba tare da dora mata takunkuman tattalin arziki na sayar mata da man fetur, wanda ya kai ga karancin makamashi a kasar.

Tsadar kayakin abinci da magunguna, kuma wannan halin tuni ya jawo tsadar rayuwa, kuma da yiyuwar haddasa kauran miliyoyin mutane daga kasar.

Baghaei ya kammala da cewa gwamnatin kasar Amurka ce da al-hakin duk abinda ya faru da mutanen kasar Cuba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted