Iran: Rundunar IRGC Sun Fara Atisayen Soje A Mashigar Ruwa Ta Hurmuz

Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran wata IRGC rashen sojojin ruwa sun fara atisayen soje wanda suka bawa suna sarrafa mashigar ruwa

Dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran wata IRGC rashen sojojin ruwa sun fara atisayen soje wanda suka bawa suna sarrafa mashigar ruwa na Hurmuz tare da amfani da kayakin zamani.

Labarin ya kara da cewa Manjo Janar Mohammad Pakpoour babban kwamandan rundunar reshen sojojin ruwa ne ya ke sanya ido a kan yadda atisayen yak e tafiya. Labarin ya kara da cewa babban manufar wannan atisayen ita ce, tabbatar da cewa sojojin ruwa na kasar sun saba da hanyoyin bayar da kariya ga mashiyar ruwan, da kuma kare ta daga makiya a duk wani lokacinda suka farwa kasar Iran da yaki. Musamman daga cikin tekun farisa ko kuma daga cikin tekun Omman.

Ya kuma kara da cewa rundunar tana shirin fuskantar duk wani haki wanda makiya zasu iya samarwa a yankin da kuma yadda zasu kunyatasu idan sun yi haka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted