Jirage Marasa Matuka Sun Kashe Mutane Akalla 28 A Sudan

Kungiyoyin kare hakkin bi’adama a kasar Sudan Sun bayyana cewa makaman Drones wadanda dakarun RSF suka cilla sun kashe mutane akalla 28 a cikin wata

Kungiyoyin kare hakkin bi’adama a kasar Sudan Sun bayyana cewa makaman Drones wadanda dakarun RSF suka cilla sun kashe mutane akalla 28 a cikin wata kasuwa a yankin Kordofan.

Shafin yanar gizo na labarai Arab news ya bayyana cewa makaman sun fada kan kasuwar Al-safiya da ke garin Sodari a lardin areawacin Kordofan a ranar Lahidan da ta gabata, sun kuma yi sanadiyyar kashe mutane akalla 28.

Labarin ya kara da cewa garin Sodari dai yana tazarar kilomita 230 daga arwacin birnin Al-Obaeid babban birnin Arewacin Kordofan wanda dakarun RSF sun dade suna sun su kwace shi daga hannun sojojin gwamnatin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted