kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’I yace hakkin iran na mallakar fasahar nukiliya na zaman lafiya wani abin gado ne wanda zai bai sa a canza daga kansa ba saboda matsin lambar siyasa
wadannan bayanai sun tabbatar da matsayin kasar iran na hakkokinta na Asasi, dake nuna cewa shirinta na makamashin nukiliya na zaman lafiya ne bai shafi batun tattaunawa ba kuma wani abin girmamawa ne na kasa mai kima.
kalaman na kakakin, amsace kai tsaye game da zargi mara tushe da kasashe masu nukiliya ke yi mata da ake amfani da su wajen kokarin kawo cikas a shirin ta na nukiliya na zaman lafiya,
haka zalika ya jaddada cewa shirin iran yana karkashin sa idon hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya , bayan dagewa da ake yi kan batun rashin bin doka da kuma ci gaba da amfani da siyasar matsin lamba, wanda ba zai hana ta cimma burinta na mallakar fasahar nukiliya na zaman lafiya ba