shugaban Ukrain Ya Bukaci Lamunin Tsaro Na Shekaru 20 Daga Amurka

shugaban kasar Ukrani Volodymyr Zelensky ya bukaci lamunin tsaro daga kasar Amurka na shekaru 20 kafin ya amince ya rattaba hannu kan yarjejeniyar Sulhi tsakaninsu

shugaban kasar Ukrani Volodymyr Zelensky ya bukaci lamunin tsaro daga kasar Amurka na shekaru 20 kafin ya amince ya rattaba hannu kan yarjejeniyar Sulhi tsakaninsu da kasar Rasha, da yake Magana a wajen taron tsaro na Munich, kafin taron sulhu na 3 tsakanin kasar Ukrain da kuma rasha da Amurka da aka shirya gudanarwa a ranar talata da laraba a birnin Ganeva,

Ana sa bangaren shugaban Amurka Donald trump yace kasar rasha tana so a kulla yarjejeniyar amma zalensky yana da wani zabi, yace yana so ya rasa wata babbar dama da ya samu,

shugaban kasar ukrain yayi ikirarin cewa kasar Amurka a yanzu ta amince da yarjejeniyar  tsaro ta shekaru 15 da ukrain, sai dai tana bukatar a tsawaita ta da kuma bayyana karin tsarin da zai fayyace irin goyon bayan da Washington za ta bai wa rundunar tsaro ta kasashen turai daka tsara idan aka cimma matsaya kan rikicin.

sai dai zalensky ya ki amincewa da bukatar trump na cewa ukrain za ta janye daga yankin Donbas a tattaunawar sulhun, kuma shugaban ukrain yace daukar wannan mataki ba zai taba yiyuwa ba, saboda yan kasar ukrani da dama suna zaune a yankin na Dambas

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted