Jaridar “Newyork Times” ta Amurkan ta buga labarin dake cewa; Gwamnatin Donald Trump ta kai mutane 9 ‘yan hijira zuwa Kamaru duk da cewa ba ‘yan asalin wannan nahiyar ta Afirka ba ne, kuma kotun kasar ta ba su kariya.
Labarin ya kara da cewa; Mutanen da su ka hada maza da mata, an dauke su ne a cikin wani jirgi daga jgarin Alexandaria dake Jahar Luisiana a ranar 14 ga watan Janairu da ya shude, an kuma dauke su da sarkoki a hannu da kafafu.
MA’aikatar harkokin cikin gidan Amurka wacce ita ce ta yi jigilar mutanen ba ta amsa tambayoyin kamfanin dillancin labarun Reuters ba akan lamarin, haka ma ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Kamaru.
Har ila yau, gwamnatin Donald Trump ba ta taba sanar da cewa ta kulla wata yarjejeniya da kasar Kamaru akan batun aike wa da ‘yan hijira ba.
Tun daga farkon Zangon mulkin Donald Trump na biyu, ya fara daukar tsauraran matakai akan ‘yan hijira da ya hada da fitar da su daga cikin Amurka zuwa wasu kasashe.
Kasashe da dama sun ki amincewa da karbar ‘yan Hijiyar da Amurkan ta so aikewa da su, daga cikinsu har da Nigeria.
Gwamnatin Nigeria ta bayyana cewa, tana fama da nata matsalolin tsaron balle ta karbi wasu ‘yan hijira da su ka kunshi masu manyan laifuka daga kasar Venezuela.