Bayan yakin duniya na biyu, turawa sun sake nufar nahiyar Afirka saboda samo dukiyar da za su sake gina kasashensu da aka rusa. Dama wannan nahiyar ce suka nufa a karnukan baya inda suka ci moriyarta. To amma a wannan karon, sake kafa mulkin mallaka irin wanda aka saba da shi ba zai yiwu ba. Domin kasashen nahiyar sun sami ‘yanci daga mulkin mallaka daya bayan daya, arzikinsu yana karkashin ikonsu. Sai dai kuma turai sun lalubo wata sabuwar hanya wacce ba ta bukatar mamaya ta soja, amma kuma a lokaci daya tsohon tasirinsu zai ci gaba. Wannan sabon makamin ba bindiga ko igwa ba ne, wani abu ne mai sauki, amma kuma ya fi su yin kisa.
Kimar albarkatun karkashin kasa na Saudiyya da ba a fara tono su ba, ta kai Dalar Amurka tiriliyan 2.5, kuma matsakaicin kudin shiga na shekara shi ne Dala dubu 54. Don haka za a iya cewa idan aka sami wata kasar da take da albarkatun karkashin kasa da suka rubanya na Saudiyya har sau goma, to ya kamata ace dukiyarta ta rubanya har sau goma. Kuma tana da dogayen hasumiyoyi mafi yawa, da ‘yan wasan kwallo mafi tsada da kuma filayen wasan kwallon kafa mafi girma.
Hotunan da kuka gani na titunan Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ne, wacce a baya ake kira da Zaire. Ita ce gaba da dukkanin kasashen duniya wajen dimbin arzikin karkashin kasa da kimarsa ta kai Dala tiriliyan 24 wadanda ba a fara dibarsu ba. Sai dai kuma matsakaicin kudin shiga shi ne Dala 600, wato kusan 1/100% na kudin shigar Saudiyya. Kuma kusan mafi yawan mutanen kasar suna rayuwa ne a cikin talauci.
Albarkatun Da Sauran Kasashen Afirka Suke Da Shi Bai Gaza Na Congo Ba. Kaso daya bisa uku (1/3 ) na ma’adanan da ake da su a duniya kamar Lithium, Nickel da Platinum suna cikin nahiyar Afirka ne. Kaso 70% na Coblat da aka sarrafa shi a duniya a 2023 an same shi ne daga kasar Congo, Idan da ba a samo su daga can ba, to da ba mu iya cajin wayoyin hannu, kwamfuta da sauran injina masu aiki da wutar lantarki ba.
A shekarar 2019, an kididdiga cewa a cikin kasashen Afirka sun fitar da ma’adanai ton biliyan daya da kudinsu ya kai dala biliyan 406. A cikin nahiyar Afirka akwai kaso 10% na mabubbugar ruwan sha da ake da su a duniya. Kuma da akwai kaso 65% na jumillar kasar noman da ake da ita a duniya a cikin nahiyar. Ahali akwai mutane da yawa a wannan nahiyar da ba su kwana a koshe.
Duk da cewa kasashen Afirka sun samu ‘yanci bayan yakin duniya na biyu, amma wannan ‘yancin na zahiri bai iya taimaka musu wajen magance talauci ba, har yanzu suna rayuwa kamar a lokacin mulkin mallaka. Kuma da dama daga cikin mutanen wannan nahiyar, kudin shigarsu na rana bai wuce Dala 2 ba, wanda hakan shi ne ma’aunin duniya na rayuwa a karkashin talauci. Fahimtar wannan batun yana da bukatuwa da mu tsallaka tekun miditireniya, domin mu isa cikin nahiyar turai.
Bayan yakin duniya na biyu, nahiyar turai ta rushe, kusan baki dayanta. Hanyar da turawan za su iya amfani da ita su sake gina nahiyar tasu ita ce, dukiyar nahiyar Afirka da suke dauka a matsayin wata taskarsu ta kashin kansu.
Sai dai a wannan karon, kasashen Afirka sun daga murya sun fada wa turawan cewa; A wannan jikon ba za ta sabu ba; abinda kuka yi a baya ya isa; A yanzu ba za mu zama masu biyan kudaden yake-yakenku ba.
Daga nan sai turawan su ka fito da wata sabuwar hanya ta wayo da za su ci gaba da sarrafa albarkatun Afirka, amma kuma su bar mutanen Afirka suna jin cewa kasashensu suna da ‘yanci, kuma ba sa karkashin mulkin mallaka.
Turawa sun kirkiro wani sabon makami, wanda sunansa bayar da lamuni. Makamki ne wanda ba ya kara, babu abubuwa masu fashewa a cikinsa, kuma kai tsaye ba ya kashe mutane.
Wannan makamin ana adana shi ne a wurare biyu; Asusun Bayar Da Lamuni Na Duniya ( IMF) da kuma Bankin Duniya (World Bank).
Bayan yakin duniya da shekara daya ne aka kafa IMF da Bankin Duniya. Manufarsu ta farko kuwa ita ce taimakawa kasashen turai da Japan da yaki ya rusa su sake gina kasashensu. Aikin Asusun IMF shi ne tsara da daidaita hanyoyin tafiyar da kasuwwanci a tsakanin kasashen da suke mambobi. Shi kuwa Bankin Duniya aikinsa shi ne bayar da bashi ga kasashe mambobi a Asusun IMF.
A tashin farko kasashen turai da na gabashin nahiyar Asiya ne suka zama mambobin Asusun, amma bayan da kasashen Afirka suka fara samun ‘yanci a tsakiyar karni na Ashirin, wannan Asusun ya jawo su saboda kwadayin samun alabrkatun da suke da su, da kuma kwadago mai saukin kudi.
Abinda IMF ya fada wa kasashen Afirka da ba su dade da samun ‘yanci ba shi ne: “ Mun san cewa kuna da ma’adanai masu daraja, amma ba ku da kayan aikin fito da su. To wannan ba matsala ba ce! Shin Kun san yadda za mu yi? Abinda ake bukata a wurinku shi ne ku zama mambobi a cikin cibiyoyinmu, za mu ba ku bashin da za ku gina cibiyoyi hako da gyara ma’adananku ku rika fitar da su zuwa waje. Idan kun sami kudade, sai ku biya mu. taken da muke bayarwa shi ne: “ Raya kasa mai dorewa, da kuma jin dadin dukkanin kasashe mambobi.”
Shawarar Asusun ta ja hankalin kasashen Afirka da ba su dade da samun ‘yanci ba, suna ganin abin nema ne ya samu. Ba tare da sun yi shakku kan wadannan alkawullan na cibiyoyin kudade ba, daya bayan daya su ka rika zama mambobi suna karbar basuka da rattaba hannu akan yarjeniyoyi masu sharudda da tsanani. Domin suna jin cewa za su karbi bashin biliyoyin Daloli cikin sauki su fitar da ma’adanan da suke da su, a karshe su biya basukan da su ka karba, sannan kuma su gina kasashensu.
A lokacin farko na biyan bashi sun fahimci cewa fara gina kasa daga farko, ba abu ne mai sauki ba. A cikin shekara daya ba za a iya magance barnar da mulkin mallaka ya yi ba na daruruwan shekaru, da kawo karshen ci bayan da ake da shi. Dukkanin basukan da kasashen Afirka suka karba daga Bankin Duniya bai wuce su kashe shi wajen gina makaranta, asibiti, titi da kuma share fagen samar da masana’antu ba. Kuma tun ma ba su karbi wani abu na azo a gani ba, sun kasa biyan bashin da bai wuce da gwmman miliyoyin Daloli ba.
Daga nan ne Asusun Bayar Da Lamuni ( IMF) ya yaye labulen wasan kwaikwayo na biyu. Jami’an wannan Asusun sun fada wa kasashen na Afirka da ba su dade da samun ‘yanci ba cewa; “ Kar ku damu. A karkashin yarjejeniyar da mu ka kulla da ku, za mu ba ku lokaci na tsawon shekara daya. To amma saboda mu sami nutsuwa akan cewa za ku iya biyan bashin farko da na biyu, za mu turo muku kwararrun mashawarta na tattalin arziki saboda su taimaka muku ku yi Dan karamin gyara a tsarin tattalin arzikin kasashenku. Yin hakan zai rage kashe kudadenku, ta yadda a kowace shekara za mu rika adana kudaden masu yawa a asusunku ta yadda za ku iya biyan basuka”
Kamar yadda yarjejeniya ta tanada, ksashen Afirka ba su da wata mafita sai aiwatar da shawarar Asusun IMF. Sai dai wannan abinda su ka kira; “Dan karamin gyara” ya bude kafar sarrafa tattalin arzikin kasashen a hannun Asusun na ( IMF). A karshe kuwa kasashen sun koma masu sayar da ma’adanai da sauran albarkatunsu ba tare da sarrafa su ba, suna kuma shigo da dukkanin kayan masarufi da suke da bukata. Batun zuba hannun jari da kere-kere da sana’o’i, ya sha kara.
Misalin wani bangare na gyare-gyaren da aka yi, shi ne rage kashe kudaden tafiyar da kasa, kara yawan kudin shiga. Amma ta yaya? Rage yawan kudaden tafiyar da kasa ya kunshi rage kasafin kudin tafiyar da ilimi, kiwon lafiya da kuma kawo karshen duk wasu kudade da ake kashewa sabdoa jin dadin al’umma. Daga nan kuma sai a kara yawan kudaden haraji. Abinda yake da muhimmanci a wurin IMF shi ne a biya bashi, bai dame su ba idan an hana mutane jin dadi, ilimi da kuma kiwon lafiya ba.
Ko kuma wadannan mashawartan na Asusun su tilasta wa kasashen na Afirka da su sayar da dukkanin kamfanoni da cibiyoyi na gwamnati da suke samun kudi, Kuma saboda kamfanoni masu zaman kansu ba su iya aiwatar da ayyuka kamar yadda ya dace, sai a bai wa kamfanonin kasashen turai hakkin tafiyar da ayyuka.
Wadannan kamfanonin na turai, sun rika fito da ma’adanan nahiyar Afirka kamar yadda suka rika yi a lokacin mulkin mallaka suna kai wa kasashen turai. Kason da suke bai wa kasashen Afirka kadan ne, saboda su yi amfani da su su biya bashin da Bankin Duniya yake bin su.
Daga lokacin da kudaden shigar mutanen Afirka ya zama kadan, ta yadda ba za su iya bayar da haraji ba, sai gwamnati ta koma buga takardun kudi saboda yin kasafin kudi. Daga nan sai darajar kudinsu ta rika faduwa kasa kowace rana. Amma a daya gefen, suna ci gaba da biyan basukan da Asusun IMF yake binsu a cikin Dala. Sai ya zama bashin da ake binsu idan aka kwatanta shi da kudin kasa, kullum karuwa yake yi.
Idan kuwa bashi ya yi katutu to zai zama babu haraji. Kuma duk da yawan albarkatun karkashin kasa da kasashen Afirka suke da su, ba zai zama ya haifar musu Da mai ido ba, balle su iya biyan bashin Bankin Duniya. Me ya kamata a yi?
A fili yake cewa wani bashin za a sake ciyowa daga Bankin Duniya domin biyan bashi da ya gabata. Sai dai sabon bashin da za a ci yana tattare da sharudda masu tsauri ta yadda Bankin Duniya da Asusun IMF za su kara shimfida ikonsu akan tattalin arzikin wannan kasa. Haka za a ci gaba da tafiya.
Me zai faru a karshe? A kasar Afirka wacce aka dakatar da dukkanin wasu ayyukan na jin dadin rayuwa ilimi da kiwon lafiya, kuma ma’aikatan wannan kasar suke samun kasa da Dala daya da rabi a rana, kowa da kowa na rayuwa a cikin bakin talauci, dukkanin kasar za ta zama wacce Asusun IMF da Bakin Duniya suke bin bashin biliyoyin daloli. Tattalin arzikin wannan kasar zai koma karkashin sarrafawar IMF, Ma’adanan karkashin kasa a karkashin ikon kamfanonin turai masu zaman kansu. Abinda wannan yake nufi shi ne an shiga wani sabon mulkin mallaka ta hanyar amfani da bashi a matsayin makami, ba tare da an zubar da jini ko aikewa da rundunar sojoji ba.
Yanzu akwai kasashe 54 a cikin nahiyar Afirka, 51 daga cikinsu suna a karkashin sarrafawar Asusun IMF Da Bankin Duniya. Har zuwa shekarar 2022 bashin da Asusun yake bin Afirka shi ne Dala biliyan 42, Bankin Duniya yana bin su kudin da sun kai Dala Tiriliyan 1.8
Taken da Asusun shi ne: “ Raya kasa mai dorewa, da kuma jin dadin dukkanin kasashe mambobi.” to amma akasin haka shi ne yake aiki akan kasashen Afirka da suke mambobi, kuma gwargwadon yadda take damfaruwa da su ne take kara talaucewa.
Watakila a yi tambaya cewa, wadannan kasashen uku da ba su taba cin basukan ba bankin duniya da IMF ba wato Libya, Botswana da Eritrea wane hali suke ciki?
Botswana ita ce kasar da ta fi samar da Dimond a duniya. Wannan kasar ba ta taba cin bashin Asusun IMF ba, kuma ba ta mayar da ma’adananta su ka zama a karkashin kamfanoni masu zaman kansu ba. Saboda haka kudaden shigarta sun karu sosai, tana kuma gina muhimman cibiyoyin raya kasa da kyautata ilimi da kiwon lafiya. Wannan ne ya sa tattalin arzikin Botswana yake da kyau gwargwado. A shekarar 2020 bashin da ake bin kasar bai wuce kaso 18% daga kudin shigarta ba. Idan aka dubi kasa kamar Congo kuwa, bashinta ya kai 15% daga kudin shigarta.
Libya kuwa, kafin turawa su ingiza ‘yan kasar su yi bore, ta kasance daya daga cikin kasashen da su ka fi arziki a Afirka, Kuma mafi kyawun tsarin kiwon lafiya, ilimi da jin dadin al’umma. Watakila ya zama abu mai jan hankali idan ku ka ji cewa kanar Gaddafi ya so ya kafa Babban Bankin Afirka saboda dukkanin kasashen nahiyar ta Afirka su kubuta daga sharrin Bankin Duniya da kuma IMF. Bai zama arashi ba da su ka jefa shi da kasar Libya a cikin bala’i. Kasa wacce take bunkasa da ci gaba ta koma wacce yaki ya daidaita. Ba goyon bayan kama-karyar Gaddafi muke yi ba amma kuma a lokaci guda ba za mu zama masu saukin kai har haka ba.
A Iran ma za mu iya ganin tasirin rashin karbar basukan Asusun ( IMF) da Bankin Duniya. Daya daga cikin dalilan da suka sa Iran ta iya jurewa matsin lamba kasashen turai na tsawon gomiya hudu, ta kuma kare cin gashin kanta duk da matsaloli nan da can, shi ne cewa basukan da ta ci daga Bankin Duniya da IMF kadan ne.
Idan Afirka tana son tseratar da kanta daga talaucin daruruwan shekaru, dole ne ta sake yi wa wannan sabon mulkin mallakar bore, wanda a cikin shekarun bayan nan an fara ganin alamunsa.
A shekarar 2024 Mutanen Kenya sun yi bore domin nuna kin amincewa da sabuwar siyasar kudaden haraji domin a biya bashin ( IMF) wanda ya kai Dala biliyan 3.2. Mutane sun mamaye ginin majalisar dokoki, suka yi taho mu gama da ‘yan sanda da ya kai ga kashe mutane 5.
A Nijar akwai wajen hako ma’adanai mai suna ( Imouraren) dake kunshe da karfen Uranium da yawansa ya kai ton dubu dari biyu ( 200,000) da hakan ya mayar da ita zama daya daga cikin mafi girman wurin samun Uranium a duniya. Daga shekarar 1971 kamfanin faransa mai suna “Orano” ya shimfida ikonsa akan wadannan ma’adanai.
Wannan kamfanin ya rika samun sanadarin Urani’um din Nijar cikin sauki yana tafiyar da cibiyoyin Nukiliyar Faransa 56. Da kuma uranium din Nijar ne Faransa take samar wa kanta kaso 65 % na wutar lantarki.
Yanzu za mu jira mu ga ko sauran kasashen Afirka za su ‘yantar da kawukansu daga sharrin turai, kamar yadda Njar ta yi, ko kuma a’a?. ko kuma za su bari ne ana cutar da su, kamar yadda aka yi wa Nijar a baya da kuma kasar Libya. Akwai wata magana da ke cewa; Da gaske ne da akwai matalauta a cikin wasu kasashen duniya, amma babu wata kasa guda daya a wannan duniyar da take matalauciya.