Kungiyar Tarayyar Afirka Tana Gabatar Da Taronta Karo Na 39 A Kasar Habasha

Taron na wannan karon yana cike da kalubale na  kisan kiyashi a sudan, hare-haren masu dauke da makamai a kasashen Nigeria, Nijar, Burkina Faso da

Taron na wannan karon yana cike da kalubale na  kisan kiyashi a sudan, hare-haren masu dauke da makamai a kasashen Nigeria, Nijar, Burkina Faso da Mali.

Shugaban tarayyar Afirka Mahmud Ali Yusufi ya bayyana damuwarsa akan rikice-rikicen da nahiyar take fuskanta da sun ci, sun ki karewa. Daga cikin wadannan rikice-rikicen da akwai na kasar Sudan, da DRC da kuma hare-haren masu ikirarin jihadi a cikin yankin Sahel.

Wata kungiya mai bin diddigin rikice-rikicen da suke faruwa a yankin na sahel ( IGC) ta bayyana cewa; A daidai wannan lokacin da ake da bukatuwa da tarayyar Afirkaf iye da kowane lokaci a baya, kungiyar tana cikin yanayi mafi rauni a tsawon tarihinta.”

Kungiyar tarayyar Afirka wacce akaa kafa a 2020, bayan da a baya ake kiranta da kungiyar kasashen Afirka, tana da mambobi 55, da a mafi yawancin lokuta suke da sabani da juna akan batutuwan da su ka shafi ci gaban nahiyar.

Wata babbar matsalar da wannan kungiyar ta tarayyar Afirka take fuskanta shi ne na kudaden tafiyar da ita, domin kaso 64% na kasafin kudinta tana samunsa ne a matsayin tallafi daga Amurka da tarayyar turai.

Daga 2020 zuwa yanzu an yi juyin Mulki har sau 10 a cikin nahiyar ta Afirka, sai dai wadanda su ka fi raunana nahiyar ta Afirka su ne na kasashen Mali,Bukina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar, saboda yadda su ka balle daga kungiyar tattalin arziki ta yammacin Afirka, ( Ecowas) su ka kafa tasu sabuwar kungiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted