An Yi Tir Da “Majalisar Zaman Lafiya” Ta Trump Na Bangare Guda

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai zaman kanta a kasar Faransa ta yi kira ga kasashen yamma su kawo karshen taimakon da suke bawa HKI

Wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai zaman kanta a kasar Faransa ta yi kira ga kasashen yamma su kawo karshen taimakon da suke bawa HKI a mamayar da takewa al-ummar Falasdinu.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar na fadar haka a zanga-zangar da ta gudanar a birnin Paris a ranar Asabar da ta gabata. Ta kuma kara da cewa “Majalisar Zaman Lafiya” ta Trump wanda ya kafa a taron Davos na tattalin arzikin da ta gabata, bata da manufar adalci a cikin al-amarin Falasdinawa tunda yan bangare guda ne kawai suke cikinta.

Saboda babu wakilan falasdinawa wadanda ake maganar yi masu adalci a majalisar. Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump wanda ya nada kansa shugaban Majalisar ya sanya Benyamin Natanyaho a matsayin mamba a cikin majalisar. Sannan babu wakilin Falasdinawa a cikinta, wannan ya nuna cewa majalisar zat aiwatar da abinda Natanyahu yake so ne kawai. Wanda kuma  manufarsa ita ce shafe al-ummar Falasdinu daga kasarsu.

Kuma kada a manta Natanyahu ne ya jagoranci kissan Falasdinawa kimani dubu 72 a Gaza kadai daga shekara ta 2023 zuwa yau. Kuma saboda haka ne kotun kasa da kasa mai hukunta manya-manyan laifuka ta duniya ICC ta fidda sammacin kama shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted