Ofishin kare hakkin bil’adama na MDD ya sanar da cewa; mayakan “RFS” sun take dokoki a lokacin da suke kokarin shimfida ikonsu a garin Al-fashar da za su ka zama laifukan yaki, da za su iya zama laifi akan jinsin bil’adama.
A wani rahoto da ofishin hukumar kare hakkin bil’adam ta MDD ta fitar, wanda ya dogara da tattaunawa da mutane fife da 140 da yakin ya yi wa illa, a Jahar Arewa da gabashin Chadi a karshen 2025, ya bayyana cewa; Adadin mutanen da aka kashe a cikin kwanaki uku na farkon shigar mayakan RSF cikin birnin na Alfashar, sun kai 6000.
Rahoton ya ce, mayakan na RSF sun kutsa cikin wannan birnin ne, da shi ne babban birnin Darfur ta Arewa, bayan da su ka killace shi na tsawon watanni 18.
Rahoton ya kuma ce; An kashe mutane 4400 ne a cikin garin na Alfashar, sai kuma wasu 1600 akan hanyar ficewa daga cikin birnin.
Wani sashe na rahoton ya ce, mayakan na RSF sun yi wa mutane kisan kiyashi, da cin zarafin mata, da garkuwa da mutane domin karbar kudaden fansa.
Wasu daga cikin laifukan da mayakan na RSF su ka tafka da akwai azabar da mutanen da su ka kama da mummunar mu’amala da mutane, da mayar da kananan yara mayaka.