‘yar majalisar Amurka Alexandria Ocasio-Cortez mai wakiltar jam’iyyar Democrat wacce take Magana a taron tsaro na “Munich’ a kasar Jamus, ta bayyana cewa; Ya kamata Amurka ta sake yin nazarin taimakon da take bai wa Isra’ila ido rufe, kamar kuma yadda ta zargi Donald Trump da kokarin sake mayar da duniya zuwa zamanin kama-karya.
Cortez ta kuma ce; Babu hankali ace a rika goyon bayan Isra’ila ido rufe, domin abu ne wanda bai dace ba.”
“Yar majalisar mai wakiltar jam’iyyar “Democrat’ ta kuma ce; A halin yanzu Donald Trump yana kokarin mayar da duniya zuwa zamanin mulkin kama karya, wanda zai sa ‘yan kama-karya su raba yankunan duniya a tsakaninsu.”
Cortez ta ce; Trump zai iya shimfida ikonsa akan rabin yankin duniya na yamma da Latin, a matsayin wani fage nashi shi kadai, sannan kuma Putin zai iya zare takobi yana yi wa nahiyar turai barazana da firgita kawayenmu. Haka kuma ta ce, idan hakan ta faru, zai zama ‘yan kama-karya ne suke iko da wasu yankuna na duniya.
A karshe ta ce, tare da cewa duniya ta shiga wani sabon yanayi, sannan duk da haka mafi yawamcin Amurkawa ba a shirye suke ba su yi watsi da tsarin demokradiyya wanda ya ginu akan dokoki.