Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wata kafar samun labarai a fadar white House na cewa jakadan Amurka a cikin al-amuran gabas ta tsakiya Teven Witscof da kuma surukin Trumo Cosner zasu gana da jami’an gwamnatin JMI a ranar Talata mai zuwa.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa, reuters bai bayyana sunan wanda ya sami labarin daga wajensa ba, amma yace za’a gudanar da taron ne a birnin Geneva na kasar Swizland.
Labarin ya kara da cewa bayan taron tawagar da Amurka zata gana da jami’an gwamnakin kasar Ukraine da Rasha don tattauna batun tsagaita wuta tsakanin kasashen biyu. A ranar 6 ga watan Fabrayru na wannan shekarar ne aka sake farfado da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran kan shirinta na makamashin Nuclia kuma bangarorin biyu sun tabbatar da cewa tattaunawar ta yi armashi.