Hukumar dake kula da kare hakkokin bil’adama ta MDD ta sanar da cewa, matakan da Amurka take dauka akan kasar cuba da su ka kunshi kayyade shigar da man fetur cikin kasar, yana yin tasiri a akan hakkokin mutanen wannan kasar.
Mai Magana da yawun Hukumar ta kare hakkin bil’adama ta MDD Marta Hurtado ta ce; Bisa la’akari da yadda harkokin kiwon lafiya da abinci da ruwa,suka dogara da man fetur da dangoginsa da ake shigar da shi daga kasashen waje, kamfarsa da ake da ita a halin yanzu a ciikin kasar, yana jefa ayyukan hidima da ake yi wa mutane cikin hatsari sosai.
Hurtado ta ce; Kera magunguna da adana su da jini da ake adanawa da sauran kayayakin kiwon lafiya suna tasirantuwa da zafi a cikin cuba, kuma fiye da kaso 80% suna da bukatuwa da lantarki, a dalilin haka yanke wutar lantarki zai yi tasiri a cikin harkokin kiwon lafiya da kuma tsafta ta daidaikun mutane.
Wasu fagagen da karancin makamashin yake yin tasiri a cikinsu sun hada da rabon kayan abinci, da hanyoyin sadarwa na al’umma, da harkar rabarwa ‘yan makaranta kayan abinci, da kuma dakunan haihuwa a cikin asibitoci. Haka nan kuma gidajen kula da tsofaffi duk suna tasirantuwa daga halin da ake ciki na karancin makamashi.
Haka nan muka ta ce shugaban hukumar ta ( OCHA) ta kare hakkin bil’adaman ta MDD ta ce, babu dalili da zai sa a halarta take hakkokin bil’adama bisa manufofi na siyasa.
Tun bayan da Amurka ta sato shugaban kasar Venezuela ne dai ta bude saboda salon takura ga kasar Cuba. A matakin farko ta hana sayarwa kasar Man fetur din kasar Venezuela, da yi wa sauran kasashen da suke sayar mata da man fetur da su shiga taitayinsu.