Abdumalik Al-Husy: Iran Ce Take Hana Makiya Cin Karensu Babu Babbaka

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi, ya bayyana cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana a matsayin ginshiki mafi girma dake bai wa

husi

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husi, ya bayyana cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana a matsayin ginshiki mafi girma dake bai wa al’umma kariya, tare da yin Ishara da matsayarta tabbatacciya wajen kalubalantar barazanar da al’ummar Musulmi suke fuskanta a wannan zamanin.

Sayyid Abdulmalik al-Husi wanda ya gabatar da jawabi a yau Juma’a ya kuma yi Ishara da halin da Falasdinu take ciki, yana mai bayyana yadda abokan gaba ‘yan sahayoniya a karkashin goyon bayan Amurka da Birtaniya suke kokarin kawar da dukkanin wasu wuraren tarihin musulunci a fadin Falasdinu.

Haka nan kuma ce; Abubuwan da abokan gaba suke yi, yana a karkashin kokarin sauya yanayin da ake ciki a yanzu da mayar da cin zarafin al’umma wani abu da aka saba da shi, da hakan yake a matsayin babban kalubale ga dukkanin musulmi.

Abdumalik al-Husi ya kuma yi Ishara da kutsen da ‘yan sahayoniya suke yi akan masallacin Kudus, amma maimakon a rika Kallon laifukan na ‘yan sahayoniya sai aka mayar da hankali akan kungiyoyin Hamas da Hizbullah ana dora musu laifi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted