Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya amince da yin afuwa wa sama da fursunoni 2,000 a yayin zagayowar cika shekaru 47 da nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar.
A bisa bukatar shugaban sashen shari’a na Iran, matakin ya shafi saki ko sassauci ga hukuncin da ake yanke ga fursunonin 2,108.
Irin wadannan matakai ana sanar da su ne a manyan bukukuwan addini da na kasa, inda shugaban sashen shari’a ke neman amincewar Jagoran don afuwa ko rage hukuncin da aka yanke wa fursunoni da suka cancanta bisa ga doka.