Iran Ta Bukaci Sakamako Na Gaggagawa A Tattaunawarta Da Amurka

Gwamnatin kasar Iran ta bukaci a gaggauta samar da sakamako a tattaunawar da ta shiga da Amurka kan shirinta na makamashin Nukliya. Kamfanin dillancin labaran

Gwamnatin kasar Iran ta bukaci a gaggauta samar da sakamako a tattaunawar da ta shiga da Amurka kan shirinta na makamashin Nukliya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’il Baghaei yana fadar haka a yau talata. Ya kuma kara da cewa batun daukewa kasar takunkuman tattalin arziki na daga cikin bukatar kasar Iran a wannan tattaunawar.

Baghaei ya kara da cewa, idan kuma a cikin halin tattaunawa Amurka ko HKI sun kuskura sun kaiwa kasar hari, to zasu gamu da maida martani mai tsanani. Ya ce shiga tattaunawa da Amurka ba saboda jinkirta duk wani harin da Amurka da kawayenta zasu kawo kan kasar ba. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ce HKI tana shiga ta fita don dulmuya gwamnatin kasar Amurka cikin yaki da kasar Iran. Don haka yayi kira ga gwamnatin Shugaba Trump ta dauki matsayin wanda zai amfani Amurka da mutanen kasar.

Baghaei ya sake nanata cewa HKI ce take haddasa mafi yawan tashe tashen hankula a yammacin Asia, kuma ta fara hakan tun kimani shekaru 80 da suka gabata. A lokacinda ta mamaye kasar Falasdinu.

A wani bangare na jawabinda a yau Talata kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ce, ba zai bayyana halin da ake ciki a tattaunawan da kasar ta shiga da Amurka a birnin Mascat ba, saboda yin haka zai shafi tattaunawar ya kuma jawo karin matsaloli. Don haka za’a bayyana yadda tattaunawar take tafiya ko kuma sakamakonta a lokacinda ya dace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted