Araqchi Ya Ce: Iran Ba Zata Taba Mika Wuya Ga Munanan Manufofi Ba

Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata taba mika kai ga barazana ko umarni ba A cikin wani sako kai tsaye kuma

Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Iran ba zata taba mika kai ga barazana ko umarni ba

A cikin wani sako kai tsaye kuma tabbatacce ga Amurka, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa: Manufofin barazanar da tarin karfin sojoji ba su yi nasara ba, kuma ba za su yi nasara wajen yin tasiri ga shawarwarin da kasar Iran ke yankewa ba, yana mai jaddada cewa: Iran ba ta mika wuya ga umarni ko kuma ta mika wuya ga matsin lamba daga waje.

Ministan Harkokin Wajen ya jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gina karfinta bisa ka’idar ‘yancin kai da kin amincewa da ikon mallaka, yana mai la’akari da wannan ka’ida a matsayin tushen manufofinta na ketare tun bayan nasarar juyin juya halin Musulunci.

Araqchi ya bayyana cewa: Tarin sojojin Amurka a yankin ba ya tsoratar da Iran, yana mai bayyana cewa, kasarsa ba ta neman mallakar makaman nukiliya. Ya bayyana cewa abin da ke damun abokan hamayyarta ba bam din nukiliya ba ne, amma ikon Iran na tsayawa tsayin daka kan manyan kasashe da kin amincewa da umarninsu.

Ya kara da cewa Iran, duk da jajircewarta ga diflomasiyya da tattaunawa, ba za ta amince da tattaunawa a karkashin barazana ko daga matsayin da aka dora mata ba, yana mai jaddada cewa abubuwan da suka faru a baya sun tabbatar da gazawar manufofin matsin lamba, kuma hanya daya tilo da za a magance duk wata matsala ita ce ta hanyar girmama juna da kuma amincewa da hakkokin al’ummar Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted