Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi watsi da kiraye kirayen mika makamai da kuma salon mika ragamar mulkin zirin ga hannun ‘yan kasashen ketare.
Wani babban jami’i a kungiyar ya yi watsi da kiraye-kirayen yana mai adawa da bukatun Amurka da Isra’ila.
Khaled Machaal, tsohon shugaban Hamas kuma darektan ofishin kungiyar na yanzu a kasashen waje, ya bayyana hakan ne a wani taro da aka yi a Doha, yana mai jaddada cewa kokarin da ake yi na alakanta kungiyoyin falasdinawan da masu aikata muggana laifuka da kuma neman su aje makammansu abu ne da “ba za a amince da shi ba” a karkashin mamayar Isra’ila.
“A game da batun mulkin, dole ne Falasdinawa su mallaki Falasdinawa.
Gaza ta mutanen Gaza ce da Falasdinu. Ba za mu yarda da duk wani iko na kasashen waje ba,” in ji shi.
Tsagaita wuta da Amurka ta yi, wadda aka amince da ita a ranar 10 ga Oktoba, 2025, ta yi alkawarin bude dukkan hanyoyin shiga Gaza, ta kuma ba da damar shigar da abinci da taimako da kuma kawo karshen yaki a madadin sakin dukkan fursunonin da Hamas ke tsare da su.
Duk da cewa Hamas ta bi yarjejeniyar, Isra’ila ta ci gaba da kai hare-harenta a Gaza kuma ta rufe yawancin hanyoyin shiga, tare da toshe shigar da muhimman kayan agaji.
Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa za a kashe kimanin dala biliyan 70 wajen sake gina zirin Gaza.